Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musuluncin Sun Fara Atisayen Soji A Shiyar Yammacin Kasar

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun fara gudanar da atisayen soji a shiyar yammacin kasar Iran An fara gudanar da atisayen soji mai girma mai suna “Manzon Allah mai girma 19” na sojojin kasa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na a Iran a shiyar yammacin kasar. Ministan Tsaron Iran ya […]
Jaridar Bloomberg Ta Fallasa Aniyar Kasashen Yammacin Turai Kan Kasar Siriya

Jaridar Bloomberg ta bayyana aniyar kasashen yammacin Turai a Siriya Jaridar Bloomberg ta yi nuni da cewa: Kungiyar tarayyar turai tana aiki tukuru domin tuntubar sabbin shugabannin kasar Siriya, a daya hannun kuma ta tanadi wa kanta kujera a kasar Siriya, gami da kokarin shawo kan sabuwar gwamnatin kasar kan rage tasirin da Rasha ke […]
Gwamnatin Rasha Ta Mayar Da Martani Ga Kasar Jamus Kan Sansanonin Sojinta A Siriya

Gwamnatin Rasha ta mayar da martani ga kalaman ministar harkokin wajen Jamus game da sansanonin Rasha a Siriya Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova, ta mayar da martani ga kalaman ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock dangane da sansanonin Rasha a Siriya, inda ta tunatar da ita cewa akwai fa […]
Muftin Oman Ya Bukaci Goyon Bayan Kungiyar Ansarullahi Ta Kasar Yemen

Muftin masarautar Oman ya yi kira ga al’ummar Yemen da sauran al’ummun kasashe da su goyi bayan jaruman Ansarullah ta Yemen Mufti na masarautar Oman, Sheikh Ahmed Al-Khalili, ya yi kira ga masu tsarkakekken zukata daga al’ummar Yemen na kwarai da dukkan al’ummun kasashe baki daya da su yi gangami wajen goyon bayan jaruman Yemen […]
Girgizar Kasa A Habasha Mai Karfin Awo 5.8 Da Gargadin Bala’in Da Zai Biyo Baya

Girgizar kasa mai karfin awo 5.8 ta afku a kasar Habasha, kuma labarai sun yi gargadin bala’i mai ban tsoro da zai biyo baya Cibiyar bincike kan yanayin kasa ta kasar Jamus ta watsa rahoton cewa: Girgizar kasa mai karfin awo 5.8 ta afku a kasar Habasha a yau Asabar. Cibiyar ta bayyana cewa: Girgizar […]
Kasashen Afirka Suna Ci Gaba Da Korar Sojojin Kasar Faransa Daga Kasashensu

Kasashen Afirka wadanda kasar Faransa tayi wa mulkin kasar suna ci gaba da korar sojojin faransa daga kasashensu. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa a cikin yan shekarun da suka gabata kasashen da kasar Faransa ta yiwa mulkin mallakar daya bayan daya suna korar sojojin faransa daga kasashensu. Kasar Mali ce […]
Saudiya Zata Taimaka Wajen Ganin An Sake Gina Kasar Siriya

Ministan harkokin wajen kasar Siriya wanda ba’a dade da nada shi ba, ya ziyarci kasar Saudiya ya kuma bayyana a shafinsa na X kan cewa Jami’an gwamnatin kasar sun bayyana masa kan cewa gwamnatin kasar a shirye take ta taimaka wajen sake gina kasar Siriya. Shafin yanar Gizo ta Arab-news ta kasar Saudiya ta bayyana […]
Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Fara Wani Shiri Na Sasantawa Da Yan Bindiga A Kananan Hukumomi 5

A cikin wani shiri wanda gwamnatin jihar Kaduna a arewacin tarayyar Najeriya tare da hadin kai da gwamnatin tarayyar kasar, sun fara tattaunawa da wasu kungiyoyi dauke da makamai wadanda kuma suke ayyukan ta’addanci a kananan hukumomi 5 a jihar, kuma sun amince su aje makamansu. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa, shirin […]
JMI Ta Bukaci Kasar Afganistan Ta Mutunta Hakkin Makobtaka Ta Kuma Saki Ruwa Koguna Biyu Da Suka Ratsa Cikin Kasar Su Kwarara Zuwa Cikin Iran

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghaei ya bayyana cewa akwai matukar bukatar kasar Afganistan ta mutunta dokokin kasa da kasa musamman wadanda suka safi rayuwar dabi’a a kasar Iran, wacce take samun rayuwarta daga wasu koguna guda biyu daga kasar ta Afganistan. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya nakalto Baghaei yana […]
Lebanon: An Jikkata Sojojin Lebanon 4 A Wani Taho Mu Gama Da Masu Dauke Da Makamai Na Kasar Syria

Sojojin Lebanon sun sanar da cewa 4 daga cikinsu sun jikkata saboda fadan da ya barke a tsakaninsu da masu dauke da makamai a yankin Ma’aribun dake Ba’alabak. Sojojin na Lebanon sun ce da marecen jiya juma’a ne aka yi taho mu-gamar wanda ba shi ne karo na farko ba. Masu dauke da makaman daga […]
Tsohon Ministan Isra’ila Ya Ce Ba Su Yi Nasara Ba A Gaza

Wani tsohon ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Haim Ramon ya ce Isra’ila ta ci kasa sosai a Gaza, kuma bayan gushewar watanni 15 ana yaki, ta kasa murkushe Hamas. Tsohon ministan na HKI ya kara da cewa; Babu wata nasara da aka samu saboda rashin cimma muhimman manufofin da aka ayyana tun da fari da su […]
Arakci: Mun Shirya Bude Tattaunawa Mai Amfani Akan Shirinmu Na Nukiliya

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulinci ta Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa; Iran a shirye take ta bude tattaunawa mai amfani akan shirinta na Nukiliya domin kai wa ga cimma yarjejeniya. Ministan harkokin wajen na Iran wanda tashar talabijin din kasar China ta CCTV ta yi hira da shi, ya ce; A shirye muke mu […]
HKI Ta Sake Keta Tsagaita Wutar Yaki A Lebanon

Sojojin HKI sun sake keta wutar yaki a kasar Lebanon ta hanyar tarwatsa da fasa gidaje a kudancin kasar. Haka nan kuma ta yi shawagi da jiragen yaki a samaniyar birnin Beirut. Kafafen watsa labarun kasar ta Lebanon sun ambaci cewa, sojojin na HKI sun kuma yi harbe-harbe a garin Marun-Ra’as dake kudancin Lebanon da […]
Miliyoyin Mutanen Yemen Sun Yi Zanga-zangar Nuna Goyon Bayan Mutanen Gaza

Miliyoyin Mutanen kasar Yemen din fito kan titunan Sanaa domin su nuna goyon bayansu ga mutanen Gaza, tare da yin kira da a kawo karshen yaki. Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen wacce ta gayyaci gangamin ta sha bayyana matsayarta na cigaba da nuna goyon baya ga mutanen Gaza da HKI take yi wa kisan kiyashi, […]
Kasar Ghana Ta Bayar Da Takardun Zama ‘Yan Kasa Ga Daruruwan Bakakan Fata Amurkawa

A cikin shekarun bayan nan kasar ta Ghana ta fito da siyasar bayar da takardun zama ‘yan kasa ga bakaken fata Amurka wadanda suke son komawa asalinsu na Afirka. Wata mata mai suna Keachia Bowers da Damond Smith sun baro Florida ta Amurka da suke rayuwa, su ka koma Ghana da zama ta bayyana jin […]