A cikin wani shiri wanda gwamnatin jihar Kaduna a arewacin tarayyar Najeriya tare da hadin kai da gwamnatin tarayyar kasar, sun fara tattaunawa da wasu kungiyoyi dauke da makamai wadanda kuma suke ayyukan ta’addanci a kananan hukumomi 5 a jihar, kuma sun amince su aje makamansu.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa, shirin zai hada da kananan hukumomiChikun, Kajuru, Kagarko, Giwa da kuma Birnin Gwari.
Labarin ya kara da cewa, wadannan yan bindiga dai, suna ayyukansu ne a kan manya-manyan tituna wadanda suka hada da titin Kaduna zuwa Abuja, Kaduna zuwa birnin Gwari, sai kuma Funtuwa zuwa Birnin Gwari.
Jaridar ta kara da cewa, a cikin kwanaki uku da ta dauka tana a cikin watan Decemban da ta gabata, tana rangadi da jami’an gwamnatin Jihar tare da hadin kai da wasu na gwamnatin tarayya, zuwa tattaunawa da wadannan yan bindiga, saboda gamsar da su kan shirin gwamnatocin na kwance damarar makamansu, da dama daga cikinsu sun bayyana anniyarsu da aiki da wadannan gwamnatoci don ajiye makamansu.
Labarin ya kara da cewa mafi yawan makaman, wadannan yan bindiga AK47. Banda haka labarin ya kara da cewa an sami rakiyar wakilai daga Tsohuwar Gaya, Chikun, Mai-daro da dajin Rimi da kuma karamar hukumar Giwa.
Labarin ya sami damar cimma yarjeniya tsakanin bangarorin, bayan sa’o’ii 72. Amma kissan Sumaila Sulaiman ko “boka” daya daga cikin yan ta’addan, ya dan jinkirta yarjeniyar don ance sojoji ne suka kashe shi.