Jaridar Bloomberg Ta Fallasa Aniyar Kasashen Yammacin Turai Kan Kasar Siriya

Jaridar Bloomberg ta bayyana aniyar kasashen yammacin Turai a Siriya Jaridar Bloomberg ta yi nuni da cewa: Kungiyar tarayyar turai tana aiki tukuru domin tuntubar

Jaridar Bloomberg ta bayyana aniyar kasashen yammacin Turai a Siriya

Jaridar Bloomberg ta yi nuni da cewa: Kungiyar tarayyar turai tana aiki tukuru domin tuntubar sabbin shugabannin kasar Siriya, a daya hannun kuma ta tanadi wa kanta kujera a kasar Siriya, gami da kokarin shawo kan sabuwar gwamnatin kasar kan rage tasirin da Rasha ke da shi a kasar ta Siriya.

A wani bangare na wannan yunkuri na Turai, ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock da takwararta na Faransa Jean-Noel Barrot sun isa birnin Damascus a ranar Juma’a domin tattaunawa da shugaban gwamnatin Siriya Abu Muhammad al-Julani.

A cewar Bloomberg, wannan ita ce ziyara ta farko da manyan jami’an kasashen yammacin duniya suka kai kasar Siriya tun bayan kifar da gwamnatin kasar, kuma tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Tarayyar Turai ke neman samar da tsarin hadin gwiwa da sabon shugaban.

Ministar harkokin wajen na Jamus ta ce, Tarayyar Turai na son taimakawa Siriya wajen samun nasarar mika mulki cikin lumana da kuma kokarin sake gina kasar, tare da jaddada cewa hanyar za ta kasance mai cike da matsala.

Baerbock ta kara da cewa: Ga Jamus alakarta da Hay’at Tahrir al-Sham tana da karin muhimmanci saboda tana son ganin wasu daga cikin ‘yan gudun hijiran Siriya kusan miliyan daya da suka yi gudun hijira zuwa Jamus a lokacin shugabancin Assad su koma kasarsu ko wasu kasashen Larabawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments