Kasashen Afirka Suna Ci Gaba Da Korar Sojojin Kasar Faransa Daga Kasashensu

Kasashen Afirka wadanda kasar Faransa tayi wa mulkin kasar suna ci gaba da korar sojojin faransa daga kasashensu. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran

Kasashen Afirka wadanda kasar Faransa tayi wa mulkin kasar suna ci gaba da korar sojojin faransa daga kasashensu.

Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa a cikin yan shekarun da suka gabata kasashen da kasar Faransa ta yiwa mulkin mallakar daya bayan daya suna korar sojojin faransa daga kasashensu.

Kasar Mali ce ta fara korar sojojin faransa daga kasarta, sannan Niger, Burkina Faso, Chad da Senegal, sannan a cikin makon da ya gabata kasar Ivory Coast ta ce tana son ganin sojojkin kasar Faransa su fice daga kasar.

Alhassan Watara shugaban kasar Ivory Coast a jawabin da yayiwa mutanen kasar, saboda shigowar sabuwar shekara, a ranar tarlatan da ta gabata, ya ce sojojin kasar Faransa za su mikawa sojojin kasar sansanin sojojinsu na BIMA da ke kusa da birnin Abidjan babban cibiyar kasuwancin kasar a cikin watan Jeneru na wannan shekara ta 2025.

A halin yanzu dai kasar Faransa tana da sojoji 600 a kasar Ivory Coast, amma kafin haka sojojin faransa 2,200 ne suke kasar ta Ivory coast.

A lokacinda kasar ta Faransa ta ga yadda ake korar sojojkinta daga kasashen Afirka, sai ta rage yawan sojojin ta a kasar Ivory coast zuwa 600. Amma a yanzun, ko 600 da suka rage za su kawo karshen zamansu a kasar a cikin wannan watan da muke ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments