Cibiyar bincike kan yanayin kasa ta kasar Jamus ta watsa rahoton cewa: Girgizar kasa mai karfin awo 5.8 ta afku a kasar Habasha a yau Asabar.
Cibiyar ta bayyana cewa: Girgizar kasar ta afku ce a nisan kilomita 142 a shiyar gabas da birnin Addis Ababa, a zurfin kasa kilomita 10.
Girgizar kasar ta biyo bayan wasu girgizar kasa da suka a afku a kasar ta Habasha a ‘yan kwanakin da suka gabata.
Wannan yanki ya fuskanci girgizar kasa mai karfin awo 5.5 a ranar Juma’ar makon da ya gabata, da kuma wasu jerin girgizar kasa da ba su da karfi fiye da talatin a cikin makonnin baya.
A cikin wannan yanayi, wani masanin ilmin kasa na kasar Masar ya yi gargadin fadada ayyukan aman wuta a kasar Habasha bayan da dutsen Dauphin ya yi a yau, la’akari da cewa girgizar kasar da Habasha ta gani a baya-bayan nan ya sa dutsen ya fashe.