Sojojin HKI sun sake keta wutar yaki a kasar Lebanon ta hanyar tarwatsa da fasa gidaje a kudancin kasar. Haka nan kuma ta yi shawagi da jiragen yaki a samaniyar birnin Beirut.
Kafafen watsa labarun kasar ta Lebanon sun ambaci cewa, sojojin na HKI sun kuma yi harbe-harbe a garin Marun-Ra’as dake kudancin Lebanon da kuma garin Hula. Wata majiyar ta kuma ce, sojojin Sahayoniyar sun harba manyan bindigogi a tsakanin garin Dalusah da kuma Bani Hayyana.
Garin Kafar-Kala yana cikin inda sojojin HKI su ka kai wa hare-hare, haka nan kuma sun kona gidaje biyu a Bani-Hayyana da amfani da motar buldoza domin bata hanyar Wadi-Saluki.
Bugu da kari jiragen yakin na HKI sun yi shawagi kamar za su kai hari a kudancin Lebanon da kuma unguwar Dhahiya dake birnin Beirut.
Kungiyar HIzbullah ta bakin ‘yan majalisarta sun gargadi HKI akan abinda take yi, tare da cewa, suna kai zuciya nesa ne, amma matukar kwanaki 60 su ka cika, kamar yadda ya zo a cikin yarjejeniyar tsagaita wuta, HKI ba ta janye ba, to za su yi mu’amala da ita a matsayin ‘yar mamaya.