Ministan harkokin wajen kasar Siriya wanda ba’a dade da nada shi ba, ya ziyarci kasar Saudiya ya kuma bayyana a shafinsa na X kan cewa Jami’an gwamnatin kasar sun bayyana masa kan cewa gwamnatin kasar a shirye take ta taimaka wajen sake gina kasar Siriya.
Shafin yanar Gizo ta Arab-news ta kasar Saudiya ta bayyana cewa Assad Hassan Al-Shibani sabon minitan harkokin wajen kasar ta Siriya, ya ce Yerima Farhan ministan harkokin wajen kasar Saudia, a ganawarsu ya bayyana cewa tabbas gwamnatin kasar Saudiya za ta taimaka wajen sake gida kasar Siriya.
Ya kuma kara da cewa, a ganawarsa da ministan tsaron kasar Saudiya Maraf Abu Qasra da kuma ministan harkokin tsaron cikin gida, Anas Khattab, da wasu jami’an gwamnatin kasar sun jadda cewa saudiya za ta taimaka.
Ziyarar ministan harkokin wajen kasar ta Siriya ta zo ne bayan da shugaba Ahmed Al-Sharaa ya yabawa kasar Saudiya a wata hirar da yayi da tashar talabijan ta kasar Saudiya wato Al-Arabiyya a cikin yan kwanakin da suka gabata.