Kasar Ghana Ta Bayar Da Takardun Zama ‘Yan Kasa Ga Daruruwan Bakakan Fata Amurkawa

A cikin shekarun bayan nan kasar ta Ghana ta fito da siyasar bayar da takardun zama ‘yan kasa ga bakaken fata Amurka wadanda suke son

A cikin shekarun bayan nan kasar ta Ghana ta fito da siyasar bayar da takardun zama ‘yan kasa ga bakaken fata Amurka wadanda suke son komawa asalinsu na Afirka.

 Wata mata mai suna Keachia Bowers da Damond Smith sun baro Florida ta Amurka da suke rayuwa, su ka koma Ghana da zama ta bayyana jin dadinta da hakan saboda tana rayuwa a cikin kasar da za ta saje da mutanenta.

Tun a 2019 ne dai kasar ta Ghana ta fito da wani shiri wanda ya bai wa suna;”Bayan Dawowa Gida” wanda yake nufin karfafa bakaken fatar dawowa da kuma tafiyar da harkokin kasuwanci a cikin kasar.

An fito da wancan shirin ne dai a waccan shekarar adaidai lokacin cika shekaru 400 da fara kai bakaken fata zuwa Amurka a matsayin bayi.

Wani ba’amurken da ya sami irin wannan takardar mai suna Dejiha Gordon ya baro Amurkan tun a 2019 inda ya tare baki daya a Ghana, ya bayyana jin dadinsa akan wannan dawowarsa Afirka.

Gordon ya ce; Da akwai jin dadi ace mutum yana da alaka da Afikra a matsayinsa na bakar fata, domin acan Amurka mun rasa duk wani abu da zai nuna ina ne tushensu na Afirka.

A cikin watan Nuwamba bakaken fata 522 su ka karbi takardaun zama ‘yan kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments