Tsohon Ministan  Isra’ila  Ya Ce Ba  Su Yi Nasara Ba A Gaza

Wani tsohon ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Haim Ramon ya ce Isra’ila ta ci kasa sosai a Gaza, kuma bayan gushewar watanni 15 ana yaki, ta

Wani tsohon ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Haim Ramon ya ce Isra’ila ta ci kasa sosai a Gaza, kuma bayan gushewar watanni 15 ana yaki, ta kasa murkushe Hamas.

Tsohon ministan na HKI ya kara da cewa; Babu wata nasara da aka samu saboda rashin cimma muhimman manufofin da aka ayyana tun da fari da su ka hada da kawo karshen Hamas, ta fuskar soja da kuma tafiyar da mulkin Gaza.

Ramun ya kuma kara da cewa; Har yanzu Hamas tana nan da karfinta na soja,kuma ita ce mai iko da yankin Gaza, duk da hare-hare masu tsanani da aka kai mata da kuma shahadar Yahya Sinwar da Isma’ila Haniyya.

Bugu da kari tsohon ministan harkokin wajen na Isra’ila ya ce: Dukkanin yankunan Gaza suna a karkashin ikon Hamas, kuma sojojinta suna nan da karfinsu, haka nan kuma tana rike da  fursunoni 100.”

Tsohon ministan na HKI ya yi ishara da yadda har yanzu Hamas take da makamai masu linzami kuma tana harba su akan Isra’ila, ya kuma kara da cewa har a wanann makon Hamas din ta harba makamai masu linzami, kai kace ba mu dauki watanni 15 muna yaki ba.

Haim Ramon ya kuma bayyana cewa,  Mun ci kasa sosai a Gaza, kuma dalilin hakan shi ne  rashin yin tsari da tanadi tun da fari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments