Miliyoyin Mutanen kasar Yemen din fito kan titunan Sanaa domin su nuna goyon bayansu ga mutanen Gaza, tare da yin kira da a kawo karshen yaki.
Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen wacce ta gayyaci gangamin ta sha bayyana matsayarta na cigaba da nuna goyon baya ga mutanen Gaza da HKI take yi wa kisan kiyashi, tare da yin kira da a kawo karshen yakin.
Sojojin Yemen suna cikin masu kai wa HKI hare-hare da zummar taya Falasidinawa yaki.