Muftin masarautar Oman ya yi kira ga al’ummar Yemen da sauran al’ummun kasashe da su goyi bayan jaruman Ansarullah ta Yemen
Mufti na masarautar Oman, Sheikh Ahmed Al-Khalili, ya yi kira ga masu tsarkakekken zukata daga al’ummar Yemen na kwarai da dukkan al’ummun kasashe baki daya da su yi gangami wajen goyon bayan jaruman Yemen masu kishi a maganganunsu na kare gaskiya da kalubalen da suke fuskanta daga rundunar zalunci da dukkan jarumtaka da azama.
Sheikh Ahmed bin Hamad Al-Khalili ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Jaruman kasar Yemen har yanzu suna ci gaba da fafutukar tabbatar da gaskiya da kuma kalubalantar dakarun zalunci da jarumtaka da ba kasafai ba ake samun irin su ba, wadanda za su iya girgiza tsaunuka masu karfi da kuma ruguza duwatsu.”
Al-Khalili ya kara da cewa: Kamar yadda ya wajaba ga daukacin al’ummar kasar Yemen na kwarai su hada kai tare da su domin samun karfin gwiwa da cimma manufofinsu, haka nan ya zama wajibi dukkanin al’ummar musulmi su karfafa goyon bayansu da tallafa musu da dukkanin abubuwan da Allah ya wadata su da shi. domin wannan hakkin musulmi ne a kan musulmi, kamar yadda Annabi {s.a.w} ya ce: “Musulmi dan uwan musulmi, ba zai zalunce shi ba kuma ba zai mika shi ga hannun zalunci ba”.