Gwamnatin Rasha Ta Mayar Da Martani Ga Kasar Jamus Kan Sansanonin Sojinta A Siriya

Gwamnatin Rasha ta mayar da martani ga kalaman ministar harkokin wajen Jamus game da sansanonin Rasha a Siriya Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen

Gwamnatin Rasha ta mayar da martani ga kalaman ministar harkokin wajen Jamus game da sansanonin Rasha a Siriya

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova, ta mayar da martani ga kalaman ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock dangane da sansanonin Rasha a Siriya, inda ta tunatar da ita cewa akwai fa sansanonin da Amirka ke da su a cikin  kasar Jamus.

Zakharova ta mayar da martanin ne a shafinta na Telegram, bayan da Ministar harkokin wajen Jamu Berbock ta ce: Lokaci ya yi da Rasha za ta janye sansanonin sojinta a Siriya.

Zakharova ta kara da cewa: Wannan shi ne abin da ya dace Ministar Harkokin Wajen Jamus ta fada dangane da sansanonin sojan Amurka da suke cikin kasar Jamus, kuma shin lokaci bai yi ba ne, da Ministan Harkokin Wajen Jamus, za ta faɗi wani abu makamancin haka ga Amurka?. A nasa bangaren shugaban sabuwar gwamnatin Siriya Ahmed Al-Shara’a ya jaddada cewa: Sabuwar gwamnatin Siriya tana da muradu masu mahimmanci tare da kasar Rasha, wadda ita ce kasa ta biyu mafi karfi a duniya, kuma tana da matukar muhimmanci, yana mai jaddada cewa sabuwar gwamnatin kasar tana sa ido kan muradun al’ummar Siriya kuma baya neman tada matsaloli da rikici da kasashen waje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments