Sojojin Lebanon sun sanar da cewa 4 daga cikinsu sun jikkata saboda fadan da ya barke a tsakaninsu da masu dauke da makamai a yankin Ma’aribun dake Ba’alabak.
Sojojin na Lebanon sun ce da marecen jiya juma’a ne aka yi taho mu-gamar wanda ba shi ne karo na farko ba. Masu dauke da makaman daga Syria ne su ka fara kai wa sojojin na Lebanon hari akan iyaka da hakan ya sa su ka mayar da martani.
Masu makaman na Syria, sun so bude wata hanyar shiga cikin Lebanon ne ta hanyar amfani da motar buldoza domin yin kutse cikin Lebanon. Sojojin Lebanon sun yi harbi a cikin iska domin gargadi, sai dai masu makaman sun mayar da wuta a kansu, kamar yadda sojojin na Lebanon su ka sanar.
Har yanzu babu cikakken bayani akan dalilin da ya sa masu dauke da makaman suke yin kutse cikin kasar ta Lebanon.