Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musuluncin Sun Fara Atisayen Soji A Shiyar Yammacin Kasar

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun fara gudanar da atisayen soji a shiyar yammacin kasar Iran An fara gudanar da atisayen soji

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun fara gudanar da atisayen soji a shiyar yammacin kasar Iran

An fara gudanar da atisayen soji mai girma mai suna “Manzon Allah mai girma 19” na sojojin kasa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na a Iran a shiyar yammacin kasar.

Ministan Tsaron Iran ya bayyana cewa: Atisayen sojin zai nuna karfin tsaron kasar da shirinta na kare kai daga duk wani harin wuce gona da iri da zata iya fuskanta.

An fara gudanar da gagarumin atisayen ne tare da canja wurin aikin Manjo Janar Mirza Kojak Khan daga filin jirgin saman Rasht zuwa filin jirgin saman Kermanshah.

A cikin wadannan sauye-sauyen da aka gudanar tare da hadin gwiwar bangarori na musamman da na dakarun kare juyin juya halin Musulunci a yankin yammacin kasar, ana amfani da yanayin ayyukan dauki cikin gaggawa.

Wannan ya hada da saurin tura sojoji da kayan aiki zuwa yankin atisayen sojin, inda Birgediya Mirza Kojak Khan ya aiwatar da matakin farko na wadannan ayyuka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments