Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulinci ta Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa; Iran a shirye take ta bude tattaunawa mai amfani akan shirinta na Nukiliya domin kai wa ga cimma yarjejeniya.
Ministan harkokin wajen na Iran wanda tashar talabijin din kasar China ta CCTV ta yi hira da shi, ya ce; A shirye muke mu sake bude tattaunawa akan shirinmu na Nukiliya, domin a baya mun dauki shekaru biyu muna tattaunawa da kasashe 6, kuma mun kai ga cimma yarjejeniya, wanda duk duniya ta dauke shi a matsayin wata nasara ta diplomasiyya.
Arakci ya kara da cewa; mun shiga waccan tattaunawar da kyakkyawar manufa,amma Amurka ce ta yi gaban kanta ta fice daga yarjejeniyar ba tare da wani dalili ba.
Har ila yau, ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya ce, har yanzu muna nan akan ka’idodin da aka yi aiki da su a wancan lokacin, wanda shi ne gina yarda da dauke takunkumi.
Haka nan kuma ya yi ishara da yadda tattaunawa da kasashen turai ba ta wuce zango daya ba, an kuma ayyana cewa za a yi zango na biyu a cikin makwanni biyu tare da kasashen turai din uku.
Dangane da sabuwar gwamnatin Amurka mai zuwa, ministan harkokin wajen na Iran ya ce; Za mu dauki mataki ne akan tsarin da ta fito da shi.
Arakci ya kuma bayyana ficewar da Amurkan ta yi daga waccan yarjejeniyar ta Nukiliya da cewa babban kuskure ne da ta yi, kuma Iran ta mayar da martani. Haka nan kuma ya ce duk da cewa a yammacin Asiya da akwai matsaloli, amma kofofin diplomasiyya ba za su taba zama a rufe ba.