Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghaei ya bayyana cewa akwai matukar bukatar kasar Afganistan ta mutunta dokokin kasa da kasa musamman wadanda suka safi rayuwar dabi’a a kasar Iran, wacce take samun rayuwarta daga wasu koguna guda biyu daga kasar ta Afganistan.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya nakalto Baghaei yana cewa gwamnatin kasar Iran tana bukatar kasar Afganistan ta bar ruwan koguna guda biyu wadanda suka tasowa daga kasar Afganistan su kwarar a dabi’arsu zuwa cikin kasar Iran. Saboda raya filayen noma da suke bukatar ruwan kogunan don rayuwa.
Ya kuma bukaci gwamnatin kasar Afganistan ta tuna da cewa akwai miliyoyin yan kasar Afganistan wadanda suke rayuwa a cikin kasar Iran, kimani shekaru 50 da suka gabata.