Isra’ila Na Ruwan Bama-bamai A Rafah Duk Da Sanarwar Shirin Tsagaita Wuta

Rahotanni daga Gaza na cewa aakarun sojin saman Isra’ila da manyan bindigogi na ruwan bama-bamai a garin Rafah yau Asabar, sa’o’i bayan da shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da taswirar Isra’ila na tsagaita wuta da Hamas a zirin Gaza. Taswirar da Isra’ila ta hada da tsagaita wuta na tsawon makonni 6 na Isra’ila, da […]

Iran Ta Bukaci Taron OIC Na Musamman Kan Rafah

Iran ta bakin Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya yi kira da a gudanar da wani taro na musamman na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC domin tattauna halin da ake ciki a zirin Gaza, da kuma kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi. “A wata tattaunawa […]

Gaza : Islamic Jihad Ta Bayyana Shakku Kan Tayin Tsagaita Wuta Da Biden Ya Sanar

Kungiyar gwagwarmaya ta Islamic Jihad ta Falasdinu ta bayyana shakku kan tayin tsagaita bude wuta da shugaban Amurka Joe Biden ya sanar, yana mai cewa “dakatar da kai hare-hare” dole ne ya hada da “janyewa na sojojin Isra’ila gaba daya” daga zirin Gaza da aka yiwa kawanya. Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata […]

Mako Na 33 Na Gangamin Goyan Bayan Falasdinu A Biritaniya

A Burtaniya daruruwan mutane ne a birane daban-daban na kasar ciki har da London suka sake gudanar da gangamin goyon bayan Falasdinu tare da yin Allah wadai da yakin da gwamnatin Isra’ila ke yi a Gaza. Masu zanga-zangar sun yi ta kwarara kan titunan biranen Birtaniya a mako na 33, inda suka nuna bacin rai […]

Iran Ta Yi Allah Wadai Da Sabbin Takunkuman Da EU Ta Kakaba mata

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da kakaba mata sabbin takunkuman karya tattalin arziki da kasashen Turai suka yi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani yayi kakkausar suka kan matakan da kungiyar tarayyar turai ta dauka na kakabawa wasu jami’ai da cibiyoyi na Iran sabbin takunkumai. Kan’ani ya kara da cewa: […]

An Gano Gawarwakin Falasdinawa Fiye Da 70 Da Sojojin Isra’ila Suka Kashe A Jabaliya

An gano gawarwakin Falasdinawa fiye da 70 da suka yi shahada da suka hada da yara 20 a Jabaliya bayan janyewar sojojin Isra’ila daga birnin Kamfanin dillancin labaran “Wafa” na Falasdinu ya watsa rahoton cewa: Tawagar motocin daukar marasa lafiya da jami’an tsaron farar hula sun gano gawarwakin Falasdinawa da dama, bayan janyewar sojojin haramtacciyar […]

Sojojin Isra’ila Sun Cika Kwanaki 239 Suna Aiwatar Da Kisan Kiyashi Kan Falasdinawa

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta cika rana ta 239 tana kaddamar da hare-haren kisan kiyashi kan Gaza Sojojin mamayar yahudawan sahayoniya suna ci gaba da aikata muggan ayyukan laifukan kisan kiyashi a Zirin Gaza, a rana ta 239 a jere, ta hanyar kai hare-hare ta sama da kuma harba makamai masu linzami kan yankunan Falasdinawa, […]

Iran: Wajibi Ne Isra’ila Ta Fuskanci Hukunci Kan Laifukan Kisan Kiyashi A Gaza

Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani  ya bayyawa cewa, dole ne Isra’ila ta fuskanci hukunci kan ayyukan kisan kare dangi da tayi kan dubban Falastinawa fararen hula a yankin Zirin Gaza. Ali Bagheri Kani ya fadi hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da firaministan Qatar cewa, inda ya […]

Hizbullah Ta Harba Rokoki a Kan Sansanonin Sojin Yahudawa A Arewacin Falastinu

Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah a kasar Lebanon ta sanar a jiya Juma’a cewa,  mayakanta sun kaddamar da wasu jerin hare-hare a kan wasu sansanonin yahudawan Haramtacciyar kasar Isra’ila. Kungiyar Hizbullah ta sake jaddada cewa ayyukanta na zuwa ne domin nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu masu tsayin daka a yankin Zirin Gaza, da kuma mayar […]