Wani Tsohon Jami’in H.K.Isra’ila Ya Ce: Yahudawa Ba Zasu Cimma Burinsu Kan Falasdinawa Ba  

Tsohon ministan haramtacciyar kasar Isra’ila ya bayyana cewa: Gwamnatin Isra’ila tana gab da shan kashi a Gaza da ba a taba ganin irinsa ba Tsohon

Tsohon ministan haramtacciyar kasar Isra’ila ya bayyana cewa: Gwamnatin Isra’ila tana gab da shan kashi a Gaza da ba a taba ganin irinsa ba

Tsohon minista a gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Haim Ramon, ya ce: Haramtacciyar kasar Isra’ila na gab da fuskantar shan kaye a manyan tsare-tsare da ba a taba ganin irinsu ba, kuma gazawar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a yakin Zirin Gaza a bayyane yake, duk kuwa da irin nasarori da aka samu a wasu dabarun da aka tsara a cewarsa.

Ramon ya kara da cewa, a wata makala da jaridar Ma’ariv ta buga a ranar Juma’a, jaridun haramtacciyar kasar Isra’ila suna boyewa jama’a cewa sojojin yahudawan sahayoniyya sun kasa murkushe abin da ya kira raunanan makiyan Isra’ila, kuma ba su da wani shiri na iya mamaye Gaza. Ya kuma yi nuni da cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta gaza cimma manufofin yakin da ta sanya a gaba.

Ramon ya kuma yi furuci da cewa: Kungiyar Hamas ta samu nasarar dawo da karfinta a duk inda sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka fice daga ciki, yana mai cewa sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi mamakin yawan mayakan ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa a Jabaliya bayan da suka ce sun fatattaki dakarun kungiyar Hamas da ke can tun a zagayen farko na kai hari kan birnin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments