Afrika Ta Kudu : Karon Farko Cikin Shakru 30 ANC, Ta Rasa Rinjaye A Majalisar Dokoki

Jam’iyyar ANC mai mulki a Afrika ta Kudu, ta rasa rinjaye a Majalisar Dokokin kasar wanda shi ne karon farko cikin shekaru talatin. A sakamakon

Jam’iyyar ANC mai mulki a Afrika ta Kudu, ta rasa rinjaye a Majalisar Dokokin kasar wanda shi ne karon farko cikin shekaru talatin.

A sakamakon kididdigar da aka fitar: Jam’iyyar ANC ce ke kan gaba amma da kashi 40.26% na kuri’un da aka kada.

Jam’iyyar Nelson Mandela ta yi asarar fiye da maki 15 idan aka kwatanta da zaben da ya gabata a shekarar 2019, lokacin data samu (57.5%).

A matsayi na biyu, jam’iyyar Democratic Alliance na da kusan kashi 22% na kuri’un, yayin da Sabuwar jam’iyyar MK ta tsohon shugaban kasar Jocob Zuma ta samu damar hawa matsayi na uku, da kusan kashi 15%, bisa ga kidayar kusan karshe.

Yanzu haka dai jagororin jam’iyyar ANC mai mulkin Afirka da Kudu sun fara tattaunawar cikin gida a kokarin da jam’iyyar ke yi kulla kawance domin kafa gwamnati.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments