Hizbullah Ta Harba Rokoki a Kan Sansanonin Sojin Yahudawa A Arewacin Falastinu

Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah a kasar Lebanon ta sanar a jiya Juma’a cewa,  mayakanta sun kaddamar da wasu jerin hare-hare a kan wasu sansanonin yahudawan

Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah a kasar Lebanon ta sanar a jiya Juma’a cewa,  mayakanta sun kaddamar da wasu jerin hare-hare a kan wasu sansanonin yahudawan Haramtacciyar kasar Isra’ila.

Kungiyar Hizbullah ta sake jaddada cewa ayyukanta na zuwa ne domin nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu masu tsayin daka a yankin Zirin Gaza, da kuma mayar da martani ga hare-haren da Isra’ila ke kaiwa garuruwa da kauyukan kudancin Labanon.

Kungiyar ta bayyana cewa mayakanta na sun kai hari a barikin Biranit bataliya ta 91 ta sojojin Isra’ila, inda suka kona wurin  tare da rusa wani bangarensa.

Hezbollah ta ce harin na mayar da martani ne ga harin da Isra’ila ta kai kan garin Maroun al-Ras da ke kudancin Lebanon.

Har ila yau mayakan na Hizbullah sun kai hari a yankin na al-Baghdadi da manyan rokoki na Burkan, inda suka yi nasarar tarwatsa wasu wurare da Isra’ila ta girke kayayyakin leken asiri, wanda kuma hakan yana zuwa ne a matsayin mayar da martani ga farmakin da Isra’ila ta kai kan garin Aitarun.

Kungiyar ta ce mayakanta sun yi luguden wuta kan matsugunin Ramot Naftali da wani makami mai linzami.

Daga baya ta tabbatar da cewa mayakanta sun kai farmaki ta sama ta hanyar amfani da  jiragen yaki marasa matuka inda suka rusa wasu wuraren harba makaman kariya na Isra’ila, da kuma inda ake sarrafa su a sansanin al-Zaoura.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments