Iran Ta Bukaci Taron OIC Na Musamman Kan Rafah

Iran ta bakin Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya yi kira da a gudanar da wani taro na musamman

Iran ta bakin Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya yi kira da a gudanar da wani taro na musamman na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC domin tattauna halin da ake ciki a zirin Gaza, da kuma kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi.

“A wata tattaunawa ta wayar tarho da Ahmed Attaf, ministan harkokin wajen kasar Aljeriya, na yi magana kan sabbin abubuwan da suka faru a yakin Gaza, da laifuffukan da gwamnatin sahyoniya ta aikata a Gaza da Rafah, da kuma hadin gwiwa tsakanin Iran da Aljeriya,” kamar yadda Bagheri Kani, ya wallafa a shafinsa na ”X”.

Iran ta kuma yaba wa Aljeriya kan kokarin gabatar da daftarin kudurin dakatar da hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ke yi.

Bagheri Kani ya kuma jaddada bukatar daukar matakin gaggawa da hadin gwiwa tsakanin kasashen musulmi domin dakile laifukan da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa, da kuma kara kai kayan agaji zuwa Gaza.

“Saboda haka, na kira wani taro na musamman na Kungiyar Hadin Kan Musulunci, kuma an yi maraba da shawarar,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa watakila zai ziyarci wasu kasashen yankin domin tattauna hanyoyin kawo karshen laifukan yahudawan sahyoniya a Gaza.

Bagheri ya ce, mai yiwuwa zai ziyarci Lebanon da Syria a mataki na farko a wannan mako domin tattauna batutuwan yankin.

Share

2 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
4 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments
Auwal suleiman
7 months ago

Alnsha Allah na Sara na man tafe

Abubakar Tukur faru
7 months ago

Allah yasa ayi lahiya aƙare lahiya.