Search
Close this search box.

Yaman ta kai hari kan jirgin ruwan Amurka USS Eisenhower a tekun Maliya da makami mai linzami

Kakakin sojin Yemen ya ce dakarun kasar sun kai hari kan jirgin ruwan Amurka USS Dwight D. Eisenhower a tekun Bahar Maliya, a matsayin martani

Kakakin sojin Yemen ya ce dakarun kasar sun kai hari kan jirgin ruwan Amurka USS Dwight D. Eisenhower a tekun Bahar Maliya, a matsayin martani ga munanan hare-haren da Amurka ta kai cikin daren Juma’a a kasar ta Yemen.

Brigadier Janar Yahya Saree a cikin wata sanarwa da aka watsa ta gidan telebijin ya ce “Rundunonin sojojin Yaman na sama da kuma na ruwa, sun kaddamar da wani hari na hadin gwiwa a kan katafaren jirgin ruwan Amurka mai dauke da jiragen sama na yaki ‘Eisenhower’ a cikin tekun Bahar Maliya.

Ya kara da cewa “An aiwatar da farmakin ne da makamai masu linzami na ballistic,  da kuam jiragen sama marasa matuka, kuma harin ya nasara wajen samun jirgin ruwan an Amurka.”

Saree ya ce, wannan martani ne ga hare-haren jiragen sama da Amurka da Birtaniya suka kai kan wasu wurare a cikin kasar Yemen,  inda suka kasha tare da jikkata mutane fararen hula hula.

Jiragen yakin Amurka da na Birtaniya sun kai hari a babban birnin kasar Yemen Sana’a da kuma yankunan Hudaydah da Taiz.

Jami’an kasar Yemen sun ce, Amurka da na Birtaniya sun kai  hare-haren nasu a Hudaidah ne a kan ginin gidan rediyo da cibiyar tsaron gabar teku da wasu jiragen ruwa na kasuwanci, inda suka kashe akalla mutane 16, tare da jikkata wasu 41 na daban.

Kakakin na rundunar sojin Yaman ya sha alwashin cewa kasar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen mayar da martani kai tsaye ga duk wani sabon hari a kan yankunan Yemen.

Sojojin Yaman suna kai hare-hare ne a kan jiragen ruwa na Isra’ila da ke bi ta cikin tekun Red Sea, da kuma hana jiragen wasu kasashe isa gabar ruwan Falastinu da yahudawa suka mamaye, inda suka sha alwashin ci gaba da yin hakan har sai Isra’ila ta dakatar da harin kisan kare dangi kan al’ummar yankin zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments