Haniyah: Isra’ila na amfani da tattaunawar sulhu don ci gaba da yin kisan gilla a Gaza

Shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Falasdinu Hamas ya bayyana cewa, da gangan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta tsawaita tattaunawar tsagaita bude wuta, domin ta

Shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Falasdinu Hamas ya bayyana cewa, da gangan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta tsawaita tattaunawar tsagaita bude wuta, domin ta ci gaba da yakin da take yi na kisan kare dangi a zirin Gaza.

Ismail Haniyeh ya fadi hakan ne yayin da yake jawabi a wani taron da aka gudanar a Beirut babban birnin kasar Labanon.

Ya kara da cewa “Bangarorin gwagwarmaya ba su yarda da zama wani bangare na wadannan dabarun ba.”

Hare-haren da sojojin Isra’ila suke kaiwa a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoban day a gabata ya zuwa yanzu, ya yi sanadiyyar yin shahadar Falastinawa akalla 36,224, galibinsu mata ne da kananan yara.

Masar da Qatar dai na shiga tsakani a tattaunawar da ake yi da nufin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a watan Nuwamba, inda Hamas ta saki 105 daga cikin yahudawan da take tsare da su.

A farkon watan Mayu, Hamas ta amince da wani kudurin sasantawa da ke ba da damar dakatar da wuce gona da iri da kuma sakin sauran mutanen da ake tsare da su daga bangarorin biyu, ammam gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi watsi da hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments