An gano gawarwakin Falasdinawa fiye da 70 da suka yi shahada da suka hada da yara 20 a Jabaliya bayan janyewar sojojin Isra’ila daga birnin
Kamfanin dillancin labaran “Wafa” na Falasdinu ya watsa rahoton cewa: Tawagar motocin daukar marasa lafiya da jami’an tsaron farar hula sun gano gawarwakin Falasdinawa da dama, bayan janyewar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila daga sansanin Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran na “Wafa” ya jaddada cewa: Ma’aikatan lafiya sun gano shahidai fiye da 70 da suka hada da kananan yara 20, a sassa daban-daban na birnin Jabaliya, kuma a halin yanzu suna ci gaba da neman mutane da dama da suka bace a cikin baraguzan gidaje, cibiyoyin mafaka, makarantu da asibitoci, wadanda ba su tsira daga luguden bama-bamai ba, har ma da asibitoci, hedkwata da cibiyoyin Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) wadanda duk hare-haren wuce gona da irin suka shafe su.