Search
Close this search box.

Gaza : Islamic Jihad Ta Bayyana Shakku Kan Tayin Tsagaita Wuta Da Biden Ya Sanar

Kungiyar gwagwarmaya ta Islamic Jihad ta Falasdinu ta bayyana shakku kan tayin tsagaita bude wuta da shugaban Amurka Joe Biden ya sanar, yana mai cewa

Kungiyar gwagwarmaya ta Islamic Jihad ta Falasdinu ta bayyana shakku kan tayin tsagaita bude wuta da shugaban Amurka Joe Biden ya sanar, yana mai cewa “dakatar da kai hare-hare” dole ne ya hada da “janyewa na sojojin Isra’ila gaba daya” daga zirin Gaza da aka yiwa kawanya.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Asabar, kwana guda bayan da Biden ya ce Isra’ila ta bayar da “taswirar kawo karshen yakin da take  a kan Falasdinawa a Gaza.  

“Muna da shakku game da abin da shugaban Amurka ya fada : Wadannan maganganun kamar gwamnatin Amurka ta canza matsayinta; Yayin da take bada cikakken goyon baya ga gwamnatin sahyoniyawan da kuma boye laifukan da take aikatawa da kuma shiga cikin hare-haren Tel Aviv a kan al’ummarmu” inji kungiyar.

Kungiyar Jihad Islami ta kuma kara jaddada cewa za ta tantance duk wata shawara da ta tabbatar da dakatar da kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar Palastinu da kuma biyan muradun Palasdinawa da kuma bukatun dakarun gwagwarmaya.

A wani jawabi daga fadar White House jiya Juma’a, Biden ya sanar da cewa, Isra’ila ta ba da taswirar kawo karshen yakin Gaza wanda ya hada da tsagaita bude wuta, da janye sojojin Isra’ila daga dukkan yankunan Gaza da ke da yawan jama’a, da sako wadanda akayi garkuwa da su domin musanya da sakin daruruwan fursunonin Falasdinu.

Ya kuma yi kira ga kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas da ta amince da tayin tsagaita bude wuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments