Search
Close this search box.

Isra’ila Na Ruwan Bama-bamai A Rafah Duk Da Sanarwar Shirin Tsagaita Wuta

Rahotanni daga Gaza na cewa aakarun sojin saman Isra’ila da manyan bindigogi na ruwan bama-bamai a garin Rafah yau Asabar, sa’o’i bayan da shugaban Amurka

Rahotanni daga Gaza na cewa aakarun sojin saman Isra’ila da manyan bindigogi na ruwan bama-bamai a garin Rafah yau Asabar, sa’o’i bayan da shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da taswirar Isra’ila na tsagaita wuta da Hamas a zirin Gaza.

Taswirar da Isra’ila ta hada da tsagaita wuta na tsawon makonni 6 na Isra’ila, da sakin mutanen da suka akayu garkuwa da su da kuma janyewar Isra’ila daga yankunan da suka fi yawan jama’a a zirin Gaza.

Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin kaddamar da wani sabon hari a unguwar Sabra da ke yammacin birnin Gaza inji Wani mai magana da yawun sojojin

Ayyukan sun fi karkata ne a yammacin birnin, a gundumar Tal al-Sultan, inda mazauna yankin suka ba da rahoton hare-hare ta sama, da harbe-harbe da tankokin yaki da kuma motocin sojoji.

Akalla mutane 95 ne aka kashe a cikin sa’o’i ashirin da hudu da suka gabata, a cewar majiyoyin Falasdinawa.

Ma’aikatar lafiya ta Hamas ta sanar da sabbin adadin mutane 36,379 da aka kashe tun fara yakin Gaza kusan watanni takwas da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments