Search
Close this search box.

Biden: Isra’ila ta ba da sabuwar mahangarta kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce Isra’ila ta yi tayin “taswirar yarjejeniya” don kawo karshen yakin da ta shafe kusan watanni takwas tana yi na

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce Isra’ila ta yi tayin “taswirar yarjejeniya” don kawo karshen yakin da ta shafe kusan watanni takwas tana yi na kisan kare dangi a kan Falasdinawa a zirin Gaza.

Biden ya sanar a wani jawabi daga fadar White House jiya Juma’a cewa, tayin na matakai uku na Isra’ila zai fara ne da wani mataki na tsawon makonni shida wanda zai sa sojojin Isra’ila su janye daga dukkan yankunan da ke da yawan jama’a a Gaza.

Wanda ya hada da: cikakken tsagaita bude wuta, janye sojojin Isra’ila daga dukkan yankunan Gaza da ke da yawan jama’a, da sakin wasu da aka yi garkuwa da su, da suka hada da mata, da tsofaffi, da wadanda suka jikkata, a madadin sakin daruruwan mutane Fursunonin Falasdinawa da Isra’ila take tsare da su.

Jawabin na Biden ya zo ne bayan Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya amince da cewa halin da ake ciki na jin kai a yankin Falasdinu ya kasance “mai tsanani.”

Shugaban na Amurka ya yi kira ga Hamas da ta amince da tayin tsagaita wuta.

“Lokaci ya yi da ya kamata a kawo karshen wannan yakin, ya kara da cewa: “Ba za mu yi harar wannan lokacin ba” don amfani da damar samun zaman lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments