Search
Close this search box.

Iran: Wajibi Ne Isra’ila Ta Fuskanci Hukunci Kan Laifukan Kisan Kiyashi A Gaza

Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani  ya bayyawa cewa, dole ne Isra’ila ta fuskanci hukunci kan ayyukan kisan kare dangi

Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani  ya bayyawa cewa, dole ne Isra’ila ta fuskanci hukunci kan ayyukan kisan kare dangi da tayi kan dubban Falastinawa fararen hula a yankin Zirin Gaza.

Ali Bagheri Kani ya fadi hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da firaministan Qatar cewa, inda ya ce, laifuffukan da Isra’ila ke yi a Gaza ba za su kasance ba tare da fuskantar hukunci na adalci ba.

Ali Bagheri Kani da Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al-Thani, wanda shi ne ministan harkokin wajen Qatar, a ranar jitya Juma’a, sun tattauna kan yadda za a bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Har ila yau, sun tattauna batutuwan baya-bayan nan a Gaza da kuma laifukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata a Rafah.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da tsanantar laifuffukan da haramtacciyar kasar Isra’ila suke aikatawa a Rafah, ministan harkokin wajen Iran na wucin gadi ya ce: Dole ne yahudawan sahyoniyawan su san cewa ci gaba da tsanantar laifuka a Gaza, ba zai tafi haka nan ba tare da sakamako ba.

Bagheri Kani ya bayyana godiyar gwamnati da al’ummar Iran bisa nuna juyayi da sakon ta’aziyya da mahukuntan kasar Qatar suka yi, musamman yadda sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya halarci janazar shugaban kasar Ebrahim Raeisi da na kasashen waje. Minister Hossein Amir-Abdollahian.

A nasa bangaren Firaministan na Qatar ya bayyana cewa, har kullum Sarkin Qatar na karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu ta fannoni daban-daban.

Ya bayyana kokarin Qatar na dakatar da yakin da kuma tsagaita bude wuta tare da aikewa da agajin gaggawa ga al’ummar Palasdinu da ke cikin mawuyacin hali.

A tattaunawar tasu, jami’an biyu sun tattauna kan batun gudanar da wani taro na musamman na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, domin yin nazari kan al’amuran da ke faruwa a Palastinu, musamman laifukan da Isra’ila ta aikata a Rafah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments