Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da kakaba mata sabbin takunkuman karya tattalin arziki da kasashen Turai suka yi
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani yayi kakkausar suka kan matakan da kungiyar tarayyar turai ta dauka na kakabawa wasu jami’ai da cibiyoyi na Iran sabbin takunkumai.
Kan’ani ya kara da cewa: Kungiyar Tarayyar Turai da ta ci gaba da yin sakaci wajen tunkarar bala’in jin kai a Gaza da Falastinu a watannin da suka gabata, don haka ta fuskanci suka daga ra’ayin jama’ar Turai da al’ummomin duniya, a maimakon mayar da hankali kan laifuffukan yaki da yahudawan sahayoniyya suka aikata a Gaza domin hukunta wannan gwamnati ta yahudawan sahayoniyya kan laifukanta, ta dauki mataki kan wasu manyan jami’an Iran da cibiyoyi masu tasiri wajen tunkarar ta’addanci da samar da ingantaccen tsaro a yankin.
Kan’ani ya ci gaba da cewa: Abin takaici ne yadda kungiyar Tarayyar Turai ta hanyar yin amfani da raunanan maganganu da zarge-zarge marasa tushe da ake maimaitawa, na ban dariya marasa asali da madogara, da yin watsi da hakikanin abin da ke faruwa a yammacin Asiya da ci gaba da gazawarta, ta sake yin amfani da wani tsohon kayan aiki da ba shi da inganci na kakaba takunkumi kan Iran, da nufin gamsar da yahudawan sahayoniyya da Amurka fiye da bukatun Tarayyar Turai da al’ummarta.