A Burtaniya daruruwan mutane ne a birane daban-daban na kasar ciki har da London suka sake gudanar da gangamin goyon bayan Falasdinu tare da yin Allah wadai da yakin da gwamnatin Isra’ila ke yi a Gaza.
Masu zanga-zangar sun yi ta kwarara kan titunan biranen Birtaniya a mako na 33, inda suka nuna bacin rai da kyama ga kisan kiyashin da gwamnatin Isra’ila ke yi wa al’ummar Falasdinu.
Kamar dai a cikin watanni 7 da suka gabata, an gudanar da gangamin goyon bayan Falasdinawa tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyin kare hakkin bil’adama da na Musulunci.
Masu zanga-zangar sun bukaci a aiwatar da umarnin kotun kasa da kasa dangane da dakatar da yakin Gaza cikin gaggawa da kuma kame masu jagorantar yakin Isra’ila, tare da jaddada wajabcin dakatar da sayar da makamai ga gwamnatin sahyoniyawan.
Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, gwamnatin Isra’ila ta kaddamar da yaki a zirin Gaza bisa abinda ta kira kakkabe kungiyar Hamas, bayan harin ba zata da kungiyar ta kai.
Isra’ila ta toshe duk wata hanya da hana shigowar kayan agajin a Gaza.