Sojojin Isra’ila Sun Cika Kwanaki 239 Suna Aiwatar Da Kisan Kiyashi Kan Falasdinawa

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta cika rana ta 239 tana kaddamar da hare-haren kisan kiyashi kan Gaza Sojojin mamayar yahudawan sahayoniya suna ci gaba da

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta cika rana ta 239 tana kaddamar da hare-haren kisan kiyashi kan Gaza

Sojojin mamayar yahudawan sahayoniya suna ci gaba da aikata muggan ayyukan laifukan kisan kiyashi a Zirin Gaza, a rana ta 239 a jere, ta hanyar kai hare-hare ta sama da kuma harba makamai masu linzami kan yankunan Falasdinawa, lamarin da ke janyo aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula musamman mata da kananan yara da kuma tsofaffi, baya ga janyo mummunan hali a harkar jin kai tare da tilastawa mutane fiye kashi 95% na al’ummar yankin hijira daga muhallinsu.

Rahotonni sun bayyana cewa: A yau Asabar, jiragen saman yakin sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya sun ci gaba da kai munanan hare-hare da lugudan bama-bamai a sassa daban-daban na Zirin Gaza, inda suke auna gidaje, wuraren tarukan ‘yan gudun hijira da kan hanyoyin shigewar jama’a, lamarin da ke janyo shahadar mutane da dama da kuma jikkatan wasu na daban.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments