Sojojin Iran Suna Da Isassun Makamai Na Yaki Na Lokaci Mai Tsawo

Kakakin sojojin JMI ya bayyana cewa JMI tana da isassun makamai wadanda zasu isa yaki da makiya na lokaci mai tsawo. Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto Burgedia Janar Mohammad Akram-Nia yana fadar haka a cikin shirin tattaunawa na radion guftegu a nan Tehran ya kuma kara da cewa, JMI ta fara […]

Iran Zata Ci Gaba Ta Tallafawa Falasdinawa Har Zuwa Kwace Qudus

A yau ne ake cika shekaru 3 da fara yakin Tufanul Al-Aksa wanda kungiyar Hamas wacce take iko da yankin Gaza, ta dorawa HKI. Wato a ranar 7 ga watan Octoban shekara 2023.don kwato kasarsu daga hannun yahudawan sahyoniyya. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Manjo Janar Ali Abdullahi babban hafsan hafsoshin […]

Yakin Tufanul Aksa Ya Farfado Da Lamarin Falasdinu A Duniya Gaba Daya

Daya daga cikin shuwagabannin Falasdinawa Khaled Al-qaddomi ya bayyana cewa yakin Tufanul Aksa wanda Falasdinawa a Gaza suka fara a rana irin ta yau shekaru 3 da suka gabata, ya farfado al-amarin falasdinawa a duniya. Kuma ya maisa al-amarin Falasdinawa a l—amari na farko a duk duniya. Kamfanin dillancin labaron ISNA na kasar Iran ya […]

Iran Ta Bukaci MDD Ta Yi Aiki Don Kawo Karshen Mamayar Kasar Lebanon

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi kira ga MDD ta yi kokarin ganin HKI ta kawo karshen mamayar da ta kewa kudancin kasar Lebanon. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da jakadan MDD na musamman kan al-amuran kasar Lebanon Jean Arnault […]

Hizbullah: Makiya Ba Za Su Iya Cimma Manufofinsu Ba

Tambarin Hizbullah

Kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hizbullah a kasar Lebanon ta fiyar da bayani dangane da zagayowar cikar shekaru 3 daga farmakin Aksa da a ciki ta bayyana cewa; gwgawarmaya za ta ci gaba kuma abokan gaba ba za su cimma muhimman manufofinsu ba.