Iran tana Da Isassun Makaman Yaki Na Lokaci Mai Tsawo

Kakakin sojojin JMI ya bayyana cewa JMI tana da isassun makamai wadanda zasu isa yaki da makiya na lokaci mai tsawo. Kamfanin dillancin labaran ISNA

Kakakin sojojin JMI ya bayyana cewa JMI tana da isassun makamai wadanda zasu isa yaki da makiya na lokaci mai tsawo.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto Burgedia Janar Mohammad Akram-Nia yana fadar haka a cikin shirin tattaunawa na radion guftegu a nan Tehran ya kuma kara da cewa, JMI ta fara samar da makamanta tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a kasar musamman bayan fara kallafaffen yaki wanda gwamnatin kasar Iraki ta dorawa kasar tare da taimakon manya manyan kasashen duniya.

Akram-nia ya kara da cewa tare da takunkuman tattalin arzikin da Amurka da kasashen turai da kawayensu suka dorawa JMI sojojin kasar sun maida hankalin wajen gina makamansu a cikin gida.

Don haka mafi yawan makaman JMI kirar cikin gida ne, sannan sun fara tara makamai don fuskantar irin wannan lokacin da kasar take ciki tun fiye da shekaru 30 da suka gabata.

Janar Akram Nio ya bayyana cewa, a halin yanzu sojojin kasar suna da isassun makamai wadanda suka hada da makamai masu linzami masu cin dogon zango kio jiragen Drone da sauransu na yaki na lokaci mai tsawo.

Daga karshe Janar Akrami Nia yace mai yuwa Iran ta kai hare hare kan makiya ba tare da su suka fara takalar kasar ba, idan ta yi hasashen ana mata barazana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted