A yau ne ake cika shekaru 3 da fara yakin Tufanul Al-Aksa wanda kungiyar Hamas wacce take iko da yankin Gaza, ta dorawa HKI. Wato a ranar 7 ga watan Octoban shekara 2023.don kwato kasarsu daga hannun yahudawan sahyoniyya.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Manjo Janar Ali Abdullahi babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran yana fadar haka a taron tunawa da kuma zagayowar ranar fara yakin a nann Tehran ko kuma taron cika shekaru uku da fara yakin.
Janar Abdullahi ya cewa fara yakin tufanal Aksa, ya rikita lissafin HKI da kawayenta a duniya musamman Amurka da kasashen turai. Y ace yakin Tufanul aksa ya gaggauta faduwa HKI kuma a halin yanzu tana kara rauni kan rauni. Y ace yakin tufanul aksa ya taimaka wajen kai HKI a halin da take ciki a yanzu.
Ya kara da cewa, HKI da kawayenta sun kashe manya manya shugabanni masu gwagwarmaya a yankin wadanda suka da Shahid Qasim Sulaiman, Sayyed Hassan Nasarallah, Esma’il Haniyya, Yahyah Sinwar da wasu da dama, amma hakan ya kara gaggauta wargajewar HKI ne kawai musamman bayan shahadarsu.
Yace shahadar Imam Shahid ya kara gaggauta faduwar haramtacciyar kasar, wanda da yardar All.. bai da nisa da awkuwa. Iran ba zata taba dakatar da tallafawa Falasdinawa ba, har zuwa faduwar gwamnatin mamaya. Wannan shi ne wasiyyar Imam Shahid kuma shi ne umurnin jagora Aya. Mojtaba Khaminaei.