Iran Ta yi Kira Ga MDD Ta Kawo Karshen Yaki a Lebanon

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi kira ga MDD ta yi kokarin ganin HKI ta kawo karshen mamayar da ta kewa kudancin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi kira ga MDD ta yi kokarin ganin HKI ta kawo karshen mamayar da ta kewa kudancin kasar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da jakadan MDD na musamman kan al-amuran kasar Lebanon Jean Arnault wanda yake ziyarar aiki a nan Tehran.

Arnault ya gabatarwa Arachi sabbin al-amura dangane da kasar Lebanon, da kuma karin bayani kan inda aka kwana dangane mamaya da kuma ci gaba da yaki a kudancin kasar Lebanon. Ya kuma kara da cewa, yana fatan nan ba da dadewaba za’a sami zaman lafiya bayan an kawo karshen yaki a kudancin kasar Lebanon.

A nashi bangaren Abbas Argchi ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, matsayin gwamnatin kasar Iran bai sawya ba. Tana son a mutunta kan iyakokin kasar Lebanon. Ya kuma bukaci MDD ta kara yin aiki don ganin sojojin HKI sun fice daga kudancin kasar Lebanon.

Jakadan MDD na musamman a kasar Lebanon har’ila yau ya gana da Majid Takhtravanci mataimakin ministan harkokin wajen kan al-amuran kasa da kasa da kuma Mahdi Shoushtari mataimakin ministan sannan darakta mai kula da al-amuran yammacin Asia a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted