Sojojin Mali Sun Kwace Garin Kidal Mai Muhimmanci Daga ‘Yan Aware

Rahotanni daka kasar Mali sun ce sojojin kasar sun yi nasarar shiga cikin garin Kidal da shimfida iko a cikinsa bayan janyewar mayakan kungiyar 'yan
sojojin mali

Rahotanni daka kasar Mali sun ce sojojin kasar sun yi nasarar shiga cikin garin Kidal da shimfida iko a cikinsa bayan janyewar mayakan kungiyar ‘yan Aware mai rajin kafa kasar” Azwad”.

Da marecen jita Talata ne dai sojojin gwamnatin kasar ta Mali su ka shiga garin na Kidal dake arewacin kasar bayan da kungiyar ‘yanto da Azwad, ta sanar da ficewa daga cikinsa da hakan yake a matsayin wata Babbar nasara ga gwamnatin Bamako da kawayenta.

Gwamnatin kasar ta Mali ta sanar da cewa tuni sojojin kasar sun fara shimfida ikonsu a cikin Kidal, kuma sannu a hankali harkokin tafiyar da Mulki  da yi wa mazaunasa hidima zai dawo.

Watanni shida da su ka gabata ne dai ‘yan awaren kungiyar Azwad su ka kwace iko da garin daga hannun sojojin gwamnati,lamarin da ya zama wani babban koma baya a yaki da masu tayar da kayar baya a kasar.

Kungiyar “Nusratul-Islami Wal Muslimin, mai alaka da alka’ida tana a matsayin babban kalubale da mahukunta Mali suke fuskanta.

Ficewar kungiyoyin daga cikin garin dai ya biyo bayan hare-haren jiragen yaki ne da sojojin Mali su ka kai tare da taimakon mayaka daga Rasha a cikin kwanaki kadan da su ka gabata.

Kamfanin dillancin labarun “Reuters’ ya nakalto wata majiya tana cewa kwanaki uku da su ka gabata ne dai sojojin na Mali da kuma Rasha su ka fara kai hare-hare akan garin Kidal da ya rusa sansanoninsu da kuma hanyoyon da suke samun taimako.

Kasar Mali dai tana samun taimako daga kasar Rasha a shekarun bayan nan a fadan da take yi da kungiyoyi Aware da kuma masu ikirarin jihadi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted