Duniya Na Bukatar Malamai Akalla Miliyan 50 Kafin Shekara 2030

Majalisar dinkin duniya ta ce akwai bukatar samar da malamai sama da miliyn 50 don koyar da ilimin sakandire

Asusun kula da ilimi, kimiyya da Ala’du na Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO ya ce ana hasashen duniya na bukatar karin malaman makaranta akalla miliyan 50 nan da shekarar 2030.

A cewar sanarwar haɗin gwiwa daga UNESCO, Hukumar ƙwadago ta Duniya (ILO), Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) da kuma ƙungiyar Education International, wannan adadi ya ƙunshi malamai miliyan 44 da ake buƙata domin cimma burin samar da ilimin firamare da sakandare ga kowa, da kuma ƙarin miliyan 6 domin ilimin matakin farko na yara ƙanana.

An fitar da wannan saƙon ne a daidai lokacin da ake bikin cika shekaru 60 da amincewa da takardar shawarwari kan Matsayin Malamai da kuma muhimmancinsu ga raywaur dan Adam.

A cewar wani rahoto da UNESCO ta fitar a watan Maris na 2026, akalla yara miliyan 273 a duniya ba sa zuwa makaranta, adadin da ke ci gaba da karuwa a shekara ta bakwai a jere.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted