Kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hizbullah a kasar Lebanon ta fiyar da bayani dangane da zagayowar cikar shekaru 3 daga farmakin Aksa da a ciki ta bayyana cewa; gwgawarmaya za ta ci gaba kuma abokan gaba ba za su cimma muhimman manufofinsu ba.
Bayanin na kungiyar Hizbullah ya kuma jaddada matsayar ci gaba da nuna goyon bayan gwgawarmayar al’ummar Falasdinu.
Bayanin ya bayyana farmakin 7 ga watan Oktoba 2023 da cewa ya sake dawo da batun Falasdinu a matsayin wanda duniya ta mayar da hankali akansa, bayan da ya kusa zama wanda za a manta da shi.
Hizbullah ta kuma ce; Ga wadanda su ka fahimci dalilin farmakin na Aksa, sun yarda da cewa; Aiki ne na jarunta da nuna kwarewa kuma halartacce musamman idan aka yi la’akari da girman zaluncin da ake yi a al’ummar Falasdinu da kokarin shafe tarihinsu da samuwarsu.
Hizbullah ta ce; Sakamakon farmakin za a dora shi akan mizamin doka da tasirinsa na siyasa ba akan mizami na karfi da girmansa ba, ko kuma a kalli kisan kiyashi da mata da kananan yara da ‘yan sahayoniya suka yi a Gaza.
Hizbullah ta kuma yi Ishara da yadda kasashen duniya su ka cika da yin zanga-zanga da gangami akan nuna kin amincewa da abubuwan da ka rika faruwa a Gaza, amma kasashen da suka fi kusa da Falasdinu su ka shiga cikin kidima domin ya kasance akasin yarjejeniyar Abraham da kulla aka da ‘yan sahayoniya da aka rika yi.
Haka nan kuma kungiyar ta Hizbullah ta jaddada rikonta da gwagwarmaya har zuwa lokacin da za a kori ‘yan mamaya daga kudancin Lebanon.