Iran Ta Gayyaci Jakadan Faransa Kan Zanga-zangar Dalibai

iran ta gayyaci jakadan faransa a iran kan muzgunawa dalibai masu zanga-zanga a paris

Rahotanni sun nuna cewa iran ta gayyaci jakadan kasar faransa a kasar iran game da matakin da yan sanda kasar suka dauka kan dalibai masu zanga-zanga , inda ta bukaci gwamnatin paris da ta bari su yi amfani da hakokinsu na gudanar da zanga-zanga da kuma gudanar da bincike kan amfani da karfi fiye da kima da yan sanda suka yi kan daliban makaranta

jakadan kasar faransa a Tehran pierre Cochard an gayyace shi zuwa ma’aikatar harkokin waje a jiya talata inda mukaddashin sakatare janar kan bangaren kare hakkin dan adam  hamid Ahmadi ya isar da sakon kasar iran  gareshi game da damuwar  Tehran na irin mummuna matakin da aka dauka kan masu zanga-zanga

Ahamdi yayi ishara ga hakkin kasar faransa na wajibi karkashin dokokin kare hakkin bil adama na riko da hakokinsu na asasi da hada da hakkin gudanar da zanga –zangar lumana, kuma yayi kira ga gwamnatin paris da ta gudanar da bincike na yin amfani da karfi da ake zargin yan sanda sun yi, kuma ta kafa wani kwamiti mai zaman kansa da zai  yi nazari kan take hakkin yin zanga-zangar  lumana da aka yi

jami’in diflomasiyar ya bayyana cewa rahotanni sun ce sama da mutane 5000 ne aka kama a lokacin zanga-zangar kuma ya nuna damuwarsa game yadda ake ce yan sanda da jami’an tsaro suka kutsa kai cikin makarantu da kuma cikin azuzuwa,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted