Masar Ta Musanta Zargin Azabtar Da Wasu Yan Jarida 6

an zargi kasar masar da azabtar da yan jarida guda 6 da ta kama da cin amanar kasa

Gwamnatin Masar ta yi watsi da zarge-zargen da ake yi mata cewa ta  azabtar da ƴan jarida da aka tsare bisa zargin cin amanar ƙasa, inda ta kira zarge-zargen a matsayin “mara tushe”.

A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan ƙasar ta bayyana zarge-zargen a matsayin “yunƙurin waɗanda abin ya shafa na guje wa tuhumar da aka yi musu”.

Wannan ya zo ne bayan da lauyoyin da ke wakiltar ƴan jaridar shida da aka kama a makon da ya gabata suka ce sun bayar da rahoton cin zarafi a lokacin da suke tsare.

A cewar lauyoyin, yawancin ƴan jaridar sun ce sun fuskanci nau’ikan azabtarwa daban-daban, ciki har da duka, tilastawa take musu ƴanci da kuma barazana a kansu da iyalansu.

Kungiyar ƴan Jarida ta Reporters Without Borders, ta yi Allah wadai da kama ƴan jaridar kuma ta yi kira da a gaggauta sakin su.

Ba wannan ne karo na farko da Masar ke fuskatra irin wannan zargi na cin zarafin manema labarai ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted