Babban sakataren janar na kungiyar hizbullah shaikh Naim Qasem yace tsoho dakatare janar din kungiyar shahid sayyid hassan Nasanrallah ya tsaya kyam a matsayin babban dan gwagwarmaya a wannnan zamani, da kuma kokarin da yayi na shinfida ginshikin gwagwarmaya a yankin,
Shaikh Qaseem ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da aka yi a kasar labanon a jiya talata na kafa gidauniyar tattara rubuce-rubuce da abubuwab gado na sayyid hassan Nasrullah, yace idan muna so mu bayyana gwagwarmaya a wannan zamani to sayyid nasarullah shi ne hakikaninta, shi ne wanda yayi aiki da dukkan yan gwagwarmaya afadin duniya don samar da hadin kai da jajircewa
Yace mamaye wasu yankuna a kudancin labanon da isra’ila ta yi na wucin gadi ne, amma da sannu za su fice daga yankunan da suka mamaye domin zaa yanto so baki daya, haka zalika yace makiya zasu bar yankin, yana mai jaddada cewa mafita tana farawa ne daga ficewar abokan gaba cikin wulakanci tare da Amurka dake da take goyon bayansu