Falasdinawa 3 Sun Yi Shahada Yayin Da Wasu Da Dama Su Ka Jikkata

Rahotanni daga zirin Gaza suna nuni da cewa; sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila suna ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki ta hanyar kai hare-hare
gawar shahidi

 Rahotanni daga zirin Gaza suna nuni da cewa; sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suna ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki ta hanyar kai hare-hare akan Falasdinawa.

Cibiyar kiwon lafiya ta “Nasri” ta sanar da karbar shahidi daya wanda ya jikkata sosai saboda harin ‘yan sahayoniya a gabashin garin Khan-Yunus.

Ita kuwa hukumar agaji ta Gaza, ta ce daya daga cikin ma’aikatanta a yi shahada alokacin da yake kokarin ceto da wadanda aka kai wa  hari a Jabaliya.

‘Yan sahayoniya sun kuma killace garin Bado, dake arewacin birnin Kudus da gidan wani dan gwagwarmaya da ake tsare da shi, Qadri Samarah da zummar rushe gidan.

  A gefe daya, yahudawa ‘yan share wuri zauna suna ci gaba da kai wa gidaje da dukiyar Falasinawa hare-hare a yammacin kogin Jordan da kuma tunbuke bishiyoyin zaitun.

Yahudawan ‘yan share wuri zauna suna barnata dukiyar falasdinawa ne a cikin yankunan da a bisa kudurorin MDD nan ne za a kafawa Faladinawa kwarya-kwaryar gwmnati.

Ita ma gwamnatin Haramtacciyar Kasar ta Yahudawa tana ci gaba da gina sabbin matsugunan ‘yan share wuri zauna duk da cewa yankunan da take yin hakan a cikinsu suna karkashin yarjejeniyar Oslo da ta amince da kafa gwamnatin Falasdinu. Masu bin diddigin abinda yake faruwa ayammacin kogin Jordan suna cewa ci gaba da barna ta ‘yan share wuri zauna da kuma gina sabbin matsugunai da ake yi ya kusa kawo karshen duk wani fata na kafa gwamnatin kwarya-kwaryar faladinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted