Himmati: Tattalin Arzikin JMI Ba Zai Karye ba

Gwamnan babbakin JMI Dr Abdunnasir Himmati ya bayyana cewa tattalin arzikin JMI ba zai karye ba, kamar yanda kasashen Amurka da HKI suka fata. Tashar

Gwamnan babbakin JMI Dr Abdunnasir Himmati ya bayyana cewa tattalin arzikin JMI ba zai karye ba, kamar yanda kasashen Amurka da HKI suka fata.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dr Himmati yana fadar haka a hirar da ta hada shi da News Chennal ta Iran a nan Tehran.  Ya kara da cewa gwamnatin kasar Amurka bayan sun kasa cimma manufofinsu a kan kasar Iran da fermata da yaki a farkon wannan shekara sun kuma kan yakin tattalin arziki, inda suka kakabawa kasar wasu karin takunkuman tattalin arziki ta tattalin arziki , wanda a fadin su cikin makonni biyu tattalin arziki JMI zai karye.

Gwamnan ya kara da cewa kamar yanda Amurka ta kasa cimma manufofinta a kan JMI a yake yaken da ta dorowa kasar, hakama da yardar All..ba zata cimma manufofinta na karya tattalin arzikin kasar ba. Ya ce a halin yanzu mun wuce kwanaki 10 daga lokacinda suka shelanta munanan takunkuman tattalin arziki, amma babu alamun tattalin arzikin kasar yana karyewa.

Himmati ya yarda cewa, mutanen Iran suna jin jiki sandiyyar takunkuman amma kuma babban bankin kasar ta shiga gaba a wannan yakin kuma wahlar ba zata kaiga karayar tattalin arziki kamar yadda makiya suke nufi ba.

Yace gwamnatin kasar iran ta tanadi dukkan abubuwan masu muhimmanci wadanda suka shafi rayuwar mutanen kasar. Don haka mutane ba zasu galabaita ba, a bangaren abinci magunguna ko ayyukan likita ko duk wata laluran da takunkuman zata jawo ba.  Ya ce da farko sun dakatar da tashin farashin kayaki a kasuwa musamman na kayakin abinci, sannan sun samar da kayaki abinci wadanda mafi yawan mutanen kasar zasu saya a farshi mai rahusa.

Dr Himmati ya bayyana cewa Amurka ba zata cimma manufofinta a wannan yakin ma kamar yadda ta fadi a yaki da makami.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted