Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasa a iran mojor Ganaral Mohsen Rezaei ya bayyana cewa Amurka ba za ta yi nasara ba a yakin tattalin arziki da ta kaddamar kan kasar Iran kamar yadda ba tayi nasara ba wajen cimma burinta a bangaren soji
Babban jami’in tsaro ya wallafa a shafinsa na X a jiya talata cewa sakataren baitil malin kasar Amurka Scott Bessent ya sha mummunan kaye a kokarin da yake yi na nuna cewa takunkumin tattalin arziki da amurka ta kakabawa iran yayi nasara sosai
A yan makwannin nan ne sakataren baitul malin Amurka Bessenta yayi wasu bayani a kafafen yada labarai dake nuna cewa matakin killacewa iran ta teku yana aiki sosai inda ya mummunan barna ga tattalin arzikin kasar iran
Daga karshe rizai yayi watsi da kalaman da Bessent yayi kuma ya jaddada matsayin iran game da mashigar Hurmuz cewa za ta bude shi ne kawai idan amurka ta amince da sharuddan iran na din din din, na kawo karshen yaki da kuma cire dukkan takunkumin da ta kakabawa iran da kuma cire killace iran da ta yi ta ruwa.