Daya daga cikin shuwagabannin Falasdinawa Khaled Al-qaddomi ya bayyana cewa yakin Tufanul Aksa wanda Falasdinawa a Gaza suka fara a rana irin ta yau shekaru 3 da suka gabata, ya farfado al-amarin falasdinawa a duniya. Kuma ya maisa al-amarin Falasdinawa a l—amari na farko a duk duniya.
Kamfanin dillancin labaron ISNA na kasar Iran ya nakalto Khaled Qaddomi yana fadar haka a taron tunawa da ciki shekaru 3 da fara yakin Tufanul Aksa a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa, All..ya yi rahama ga shahida yahayah Sinwar shugaban kungiyar Hamas a lokacin yace, zasu sauya gabas ta tsakiya a wannan yakin, sai gashi abinda yake magana a kai ya tabbata, yakin tufanul Aksa ta sauya gabas ta tsakiya kuma ta sauya hatta duniya gaba dayanta.
Don haka ranar 7 ga watan Octoba rana ce babban ga al-ummar Falasdinu ga kuma sauran duk wanda ya damu da al-amarin Falasdinawa a duniya cikin musulmi ko kuma wadanda ba musulmi ba. Ya ce a halin yanzu kasashen Turai da Amurka sun tasirintu da yakin Tufanul Aksa. Sun rasa kuma yanda zasu da isa.
Ya ce Natanyahu yana tsammanin zai warware al-amarin Falasdinawa ta kashe su sanan ya kyautata dangantaka da kasashen larabawa da musulmi da haka kuma maganar zata wuce. Amma yakin Tufanul Aksa ta lalata al-amarunsu da kuma mummunan shirinsu.
Tufanul Aksa ta tabbatar da cewa ana iya samun nasara a kan HKI duk tare da cewa ta mallaki makamai mafi karfi da yawa a duniya.