Sheikh Ibrahim Zakzaky Ya Girmam ‘Ya’yan Shahidan Harkar Musulunci

A jiya Juma’a ne Sheikh Ibrahim Yakubu El-Zakzaky ya girmama ilayan shahidai almajiransa da su ka rasa rayukansa a shekarun baya. A jawabin da ya yi, Sheik Ibrahim El-zakzaky ya yi kira ga ‘ya’yan shahidan da su cigaba da tafiya akan tafarkin iyayensu shahidai na fada da zalunci’ kamar yadda ya ambata. Sheikh Zakzaky ya […]
Amurka Ta Aike Da ‘Yan –Ci-Rani Ba Bisa Ka’ida Ba Zuwa Guantanamo

Jiragen yakin Amurka biyu dauke da ‘yan gudun hijira da su ka shiga kasar ba tare da izini ba, sun sauka Guantanamo. A ranar Juma’a ne dai jiragen sojan Amurkan biyu su ka dauki yan ci-ranin da aka kora daga kasar zuwa tsibirin Guantanamo mai bakin suna. Jirgin farko mai dauke da ‘yan ci-ranin 79 […]
Iran Za Ta Kaddamar Da Jirgin Kasa Mai Tsananin Sauri Tsakanin Tehran Da Mashhad

Babban darekta na zartar da manyan ayyuka na kamfanin jirgin kasa Ali Kazemi ya bayyana cewa za a kaddamar jirgin kasa mai matukar sauri a tsakanin birnin Tehran zuwa birnin Mashahad a mako mai zuwa. Darektan hukumar jiragen kasar na birnin Qum ya kara da cewa, idan aka shimfida hanyar wannan jirgin kasan mai hanzari […]
Fursuna Mafi Dadewa A Kurkukun HKI Ya Sami ‘Yanci A Musayar Fursunoni Tsakanin Hamas Da “Yan Sahayoniya

A yau Asabar ne HKI ta saki Ra’id Sa’adi wanda ya yi zaman kaso na tsawon shekaru 36, a karkashin musayar da aka yi a tsakanin kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas da kuma HKI. ‘Yan Sahayoniya sun kama Ra’id Sa’adi ne a 1987, tare da yanke masa zaman kurkuku na rai da dai, har sau […]
Sojojin Lebanon: Isra’ila Tana Shirin Zaman Sojan Badakkare A Kudancin Lebanon

Rundunar sojan kasar Lebanon ta sanar da cewa sojojin abokan gaba Isra’ila jan jiki wajen janyewa daga kudancin Lebanon da hakan yake hana su sojojin Lebanon din shiga yankunan yankin. Sanarwar sojojin Lebanon din da su ka fitar a yau Asabar, ta amabci cewa; A daidai lokacin da kwakani 60 suke cika daga tsagaita wutar […]
Hamas Ta Saki ‘Yan Isra’ila Hudu

A wani na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da suka cimma, kungiyar Hamas ta saki wasu ‘yan Isra’ila hudu a wannan Asabar yayin da ake dakon gwamnatin Tel-Aviv ta saki Falasdinawa 200 a na ta bangare. Kungiyar Hamas ta bayyana sunayen wasu mata hudu sojojin Isra’ila da ta saki yau Asabar, kuma tuni ta mika […]
Amurka Ta Katse Tallafinta Ga Kasashe Ban Da Isra’ila Da Masar

Gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump ta sanar da dakatar da fitar da wani tallafi na kudade ga kasashen waje, in ban da na kawarta Isra’ila da kuma kasar Masar. A cikin wata sanarwa da sabon sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya fitar ya umurci manyan jami’ai da su “tabbatar da cewa, sun bi umurnin”. […]
Gambia : Yahya Jammeh Ya Bayyana Aniyarsa Ta Komawa Gida

Tsohon shugaban kasar Gambia, Yahya Jammeh ya bayyana aniyarsa ta komawa kasar. A wani sakon murya da ya aike wa magoya bayansa, Jammeh da ya mulki Gambia na tsawon shekaru 23 ya ce yana so ya koma kasarsa da kuma jan ragamar shugabancin jam’iyyarsa ta APRC. “In shaa Allahu zan dawo”. ‘’Kuna tsammanin ina tsoron […]
Cinikin Waje Na Iran Ya Samu Tagomashi A 2024

Sha’anin cinikayya daga waje na Iran ya samu tagomashi a a shekarar 2024 idan aka kwatanta da shekarar data gabatace ta. Cinikin waje na Iran ya kai dala biliyan 126 a cikin watanni 10 na shekarar data gabata.. A cewar hukumar kwastam ta Iran, cinikin kayayakin da ba na man fetur ba na Iran ya […]
Kasar Iran ta Yi Watsi Da Zargin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kanta

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da zarge-zargen da haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi kanta A cikin wata wasika da ya aike wa shugaban kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da babban sakataren Majalisar, jakadan Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’id Irawani ya yi watsi da zargin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila […]
Majalisar Malaman Musulunci Ta Kasar Lebanon Ta Bukaci Janyewar Sojojin Isra’ila Daga Kudancin Kasar

Majalisar malaman Musulunci ta kasar Lebanon ta bayyana cewa: Rashin janyewar sojojin mamayar Isra’ila daga yankin kudancin Lebanon, shelanta yaki ne akan kasar Majalisar malaman Musulunci ta kasar Lebanon a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta yi tsokaci kan ci gaban siyasar kasar Lebanon da ma yankin Gabas ta Tsakiya, ta yi nuni da […]
Kungiyoyin Falasdinawa Sun Yi Tir Da Sanya Sunan Kungiyar Ansarullah Ta Yemen Cikin Kungiyoyin ‘Yan Ta’adda

Kungiyoyin Falasdinawa sun bayyana cewa: Sanya kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda da Amurka ta yi alama ce ta girman kungiyar da alfaharin Gaza Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun jaddada cikakken goyon bayansu ga kasar Yemen da bangaren kungiyar Ansarullah kan duk wani nau’in hari da Amurka da ‘yan sahayoniyya suke kai musu, […]
Kasar Rasha Ta Gindaya Sharadin Fara Zama Da Gwamnatin Amurka

Kasar Rasha ta sanar da sharadin komawa ga zaman tattaunawa da Amurka Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya jaddada cewa: Farfado da kyakkyawar alaka tsakanin kasashen Rasha da Amurka ya dogara ne kan yadda Amurka ta kare masalaha da muradun Rasha. Lavrov ya bayyana haka ne a yayin wani taron manema labarai cewa: “Idan […]
Sojojin Sudan Sun ‘Yantar Da Wasu Sansanoninsu Daga Mayakan Dakarun Kai Daukin Gaggawa

Sojojin Sudan sun ‘yantar da babban hedikwatar rundunar sojin kasar da mayakan dakarun kai daukin gaggawa suka killace ta tsawon lokaci Rahotonni sun bayyana cewa: Sojojin Sudan sun kawo karshen killace babbar hedikwatar rundunar sojin kasar da ke birnin Khartoum fadar mulkin kasar daga dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka yi tsawon […]