Babban darekta na zartar da manyan ayyuka na kamfanin jirgin kasa Ali Kazemi ya bayyana cewa za a kaddamar jirgin kasa mai matukar sauri a tsakanin birnin Tehran zuwa birnin Mashahad a mako mai zuwa.
Darektan hukumar jiragen kasar na birnin Qum ya kara da cewa, idan aka shimfida hanyar wannan jirgin kasan mai hanzari za a rika isa Mashahd daga Tehran a cikin sa’oi 8 da mintuna 20 maimakon fiye da sa’aoi 12.
Kazemi ya kara da cewa, daya daga cikin muhimman manufofin jamhuriyar musulunci ta Iran shi ne hada hanyoyin kai da komowa a tsakanin muhimman biranen kasar da su ka hada da masu masana’antu.