Majalisar Malaman Musulunci Ta Kasar Lebanon Ta Bukaci Janyewar Sojojin Isra’ila Daga Kudancin Kasar

Majalisar malaman Musulunci ta kasar Lebanon ta bayyana cewa: Rashin janyewar sojojin mamayar Isra’ila daga yankin kudancin Lebanon,  shelanta yaki ne akan kasar Majalisar malaman

Majalisar malaman Musulunci ta kasar Lebanon ta bayyana cewa: Rashin janyewar sojojin mamayar Isra’ila daga yankin kudancin Lebanon,  shelanta yaki ne akan kasar

Majalisar malaman Musulunci ta kasar Lebanon a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta yi tsokaci kan ci gaban siyasar kasar Lebanon da ma yankin Gabas ta Tsakiya, ta yi nuni da abin da ofishin fira ministan mamayar Isra’ila ya sanar cewa: Ba zasu fice daga kasar ta Lebanon ba, bayan cikan wa’adin kwanaki sittin, bisa la’akari da cewa, sojojin kasar Lebanon ba su cika dukkanin sharuddan yarjejeniyar da aka cimma ba, saboda mayakan kungiyar Hizbullah ba su janye daga kudancin Litania ba. Don haka sojojin mamayar Isra’ila za su ci gaba da zama na tsawon lokaci a wasu yankunan kudancin Lebanon tare da hadin gwiwar Amurka.

Majalisar malaman Musulunci ta Lebanon ta yi la’akari da cewa: “Wannan sanarwa ta gwamnatin mamayar Isra’ila tana matsayin shelanta yaki ne kan kasar Lebanon, kuma ya zama dole gwamnatin Lebanon ta taka gagarumar rawa ta hanyar neman kasashen da suka shiga tsakanin wajen cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta, musamman Amurka, kan su tilasta ganin an mutunta alkawurran da aka dauka a yayin cimma yarjejeniyar dakatar da bude wutar. Idan kuma ba ta yi haka ba, kasar Lebanon, a bisa yarjejeniyar da ta bai wa kowane bangare ‘yancin kare kansa, tana da hakki, kuma wajibin kare kansa, tare da ‘yancin kasarta daga duk wani matakin mamaya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments