Sojojin Sudan Sun ‘Yantar Da Wasu Sansanoninsu Daga Mayakan Dakarun Kai Daukin Gaggawa

Sojojin Sudan sun ‘yantar da babban hedikwatar rundunar sojin kasar da mayakan dakarun kai daukin gaggawa suka killace ta tsawon lokaci Rahotonni sun bayyana cewa:

Sojojin Sudan sun ‘yantar da babban hedikwatar rundunar sojin kasar da mayakan dakarun kai daukin gaggawa suka killace ta tsawon lokaci

Rahotonni sun bayyana cewa: Sojojin Sudan sun kawo karshen killace babbar hedikwatar rundunar sojin kasar da ke birnin Khartoum fadar mulkin kasar daga dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka yi tsawon shekara daya da rabi

Haka nan majiyar rundunar sojin kasar ta Sudan ta sanar da cewa: Sojoji sun ‘yantar da sansanin ajiye makamai na birnin Khartoum Bahri, bayan fadan da aka yi a tsakanin bangarorin biyu a birnin na Khartoum Bahri.

Babban kwamandan rundunar sojin kasar a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce: Dakarunsu sun kammala kashi na biyu na ayyukansu inda suka gana da sojojin da ke tsare da wasu yankuna na birnin Khartoum Bahri tare da dakarun da ke babban hedikwatar rundunar birnin.

Sanarwar ta kara da cewa: Rundunar sojin Sudan tana taya sojojinta a dukkan fagagen da suke sumun nasara, tare da fatattakar mayakan ‘yan kungiyar ta’addanci ta Al-Dagalo daga birnin El- Fasher fadar mulkin Darfur ta Arewa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments