A yau Asabar ne HKI ta saki Ra’id Sa’adi wanda ya yi zaman kaso na tsawon shekaru 36, a karkashin musayar da aka yi a tsakanin kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas da kuma HKI.
‘Yan Sahayoniya sun kama Ra’id Sa’adi ne a 1987, tare da yanke masa zaman kurkuku na rai da dai, har sau biyu, da kuma Karin shekaru 20 a kai.
Laifin Sa’adi shi ne zamansa memba a cikin kungiyar Jihadul-Islam, da kuma kashe sojojin mamaya guda biyu.
A lokacin da yake zaune a kurkuku ya rasa da dama daga cikin ‘yan’uwansa da su ka hada da mahaifiyarsa da ta rasu a 2014, da kuma ‘yar’uwarsa shakikiya, sai kuma mahaifinsa da ya rasa maganansa.
An haifi Ra’id Muhammad Sharif al-Sa’adi ne a 20 ga watan Febrairu na 1966 a garin Silatul-Harisiyyah dake yammacin garin Jenin dake, kuma a can ne ya yi karatunsa na sakandire da kuma ilimin zamantakewa a jami’ar Kudus. Har ila yau ya hardace alkur’ani mai girma.
Saboda nau’oi daban-daban na azabtarwa da ya fuskanta, yana fama da cutuka masu hatsari, kuma an sha yi masa aikin fida a lokacin yana zaune ya kurkuku. Bayan rasuwar mahaifiyar tashi ya rubuta littafi mai take: “ Ummy Maryamul-Falasdiniyya” da ya kyautar da shi gare ta da kuma iyaye mata da ‘ya’yansu suke rayuwa a cikin kurkuku.